Tarayyar Amurka
Tarayyar Amurka, (da Turanci United States of America) ko Amurka ko Amurika ko Amerika ko Haɗin kan Jahohin Amurka jamhoriya ce da ta haɗa jihohi guda hamsin (50), da faɗin ƙasa da manya manyan ƙasashe masu cin gashin kansu guda biyar. Akwai kuma wasu yankunan marasa ƴanci guda 11, da kuma wasu kananan tsibirai guda 9. Amerika na da faɗin ƙasa da takai sukwaya mil miliyan 3.8 (wato kilo mita 9.8), da kuma adadin mutane miliyan 325, ƙasar amurka itace ƙasa ta uku ko ta huɗu wajen yawan faɗin ƙasa kuma ta uku wajen yawan mutane. Birnin tarayyar ƙasar shine Washinton Gundumar Kolombiya, birni mafi yawan jama'a da girma kuma shine New York. Jihar Alaska itace a gefen kwanar arewa maso yamma na arewacin Amurka, iyaka da ƙasar Kanada daga gabas. Rushewar Tarayyar Soviets yayi sanadiyyar zaman Amurka ƙasa mafi ƙarfin iko a duniya kuma Amurka itace ƙasar da ta gabatar da mulkin demokradiyya a ƙasashen duniya da dama
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Mutanen Paleo-Indian ne suka yi hijira daga ƙasar Rasha zuwa Arewacin Amurka aƙalla shekaru 15,000 da suka wuce. Mulkin mallakar turawan Birtaniya ya fara ne daga ƙarni na 16. juyin juya halin Amurka ya fara ne a shekara ta 1776. An kawo ƙarshen yaƙin ne a shekara ta 1783 bayan kafuwar Tarayyar Amurka. Amurka na amfani da Kundin tsarin mulki na shekara ta 1788, wanda aka sama suna The bill of right. Ƙasar Amurka itace ƙasa mafi ƙarfin iko a Duniya tun bayan rushewar Taraiyar Soviets. Kuma itace ƙasar da ta gabatar da mulkin demokradiyya a wasu daga ƙasashen dake duniya.
ƙasar Amurka itace ta gabatar da Majalisar Dinkin Duniya, Bankin Duniya, da sauran manyan ƙungiyoyin duniya.Amurka itace ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziƙin duniya da siyasa da kuma al'adu.
Tarihin Amurka
gyara sashesunana Yusuf sahabi,
Ƙarin Bayani
gyara sashe- Jihohi a Tarayyar Amurka
- Majalisar Ɗinkin Duniya
- Kyautar Nobel
- Kungiyar Agaji Ta Red Cross Ta Duniya
Wikimedia Commons on Tarayyar Amurka